Hausa News

Zan ci gaba da biyan albashin korarrun ƴan sandan da ke gadi na — Rarara

Add

Shahararren mawakin siyasar nan, Dauda Kahutu Rarara, ya yi alkawarin daukar nauyin ƴan sandan nan guda uku da rundunar ƴansandan Nijeriya ta kora bisa laifin amfani da bindiga ba bisa ka’ida ba da kuma rashin sanin makamar aiki.

Jaridar DAILY NIGERIAN ta ruwaito cewa ƴansandan da ke tsaron Rarara sun shiga cikin matsala bayan wani faifan bidiyo da ya nuna yadda suke harba bindiga a sama, a wani mataki na nuna karfin tuwo ga abokan hamayyar mawakin.

Rundunar ta ce bayan bincike, ta samu Insp. Dahiru Shuaibu, Sgt. Abdullahi Badamasi da Sgt. Isah Danladi da laifi kuma daga baya aka kore su.

Da ya ke magantuwa a kan korar da aka yi musu, mawakin ya sha alwashin ci gaba da sauke nauyin da ke kan su da suka hada da biyan su albashinsu na wata- wata.

Sai dai ya ce ya na roko ga rundunar da ta yi musu sassauci.

“Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta kori jami’an tsaro na. Bayan sun sanar da ni sai na tambaye su ko nawa ne albashin su a ’yan sandan Najeriya, sai suka gaya mi ni.

“Kuma na yi masu alkawari cewa, daga yanzu, zan ci gaba da biyan su albashin da da rundunar ƴansanda ke biyan su.

“Sun daukaka kara kan korar da aka yi musu, kuma idan sun yi nasara, za a iya mayar da su bakin aiki, idan kuma a karshe  hakan bai faru ba, zan ci gaba da biyan su.

“Na tuntubi mutane daban-daban domin su shiga maganar, tun kafin a kore su, amma duk da shiga tsakani da rokon da na yi wa ƴansanda, amma rundunar ta dage kan korar su,” in ji Rarara.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button