Hausa News

Za A Fara Kamen Samari Da ’Yan Mata Masu Hira Lokacin Sallar Tahajjud A Kano

Add

Hukumar ta ce za ta baza dakarunta a duk fadin jihar lokacin sallar

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta gargadi samari da ’yan matan da ke fakewa da Sallar Tahajjud wajen yin hirar soyayya da su daina ko su hadu da fushin dakarunta.

Hukumar ta kuma sanar da baza dakarunta na kar-ta-kwana a wuraren da jama’a ke gudanar da sallar domin samar da tsaro da magance dabi’ar kwacen waya a lokutun sallar dare.

Babban kwamanda hukumar a Jihar, Dokta Harun Ibn Sina ne ya bayyana hakan a hukumar da ke Kano, jim kadan da kammala ganawa da dakarun da za su aiwatar da aikin, kamar yadda wata sanarwa da Kakakin hukumar, Lawan Ibrahim Fagge, ta rawaito ranar Laraba.

A cewar Babban Kwamandan, a bana hukumar ta fadada aiyukan samar da tsaro da sa ido akan masu kai komo a dukkan wuraren ibadar ne bayan kyakkyawar nasarar da ta samu a bara.

Ya ce a bana, shirin ya hadar da dukkan Kananan Hukumomin Jihar guda 44 tare da da nufin samun nasara.

Ya kuma shawarci dukkan Musulmi da su yawaita, addu’o’in samun zaman lafiya a fadin Jihar da ma kasa baki daya, tare da addu’ar fardowar tattalin arziki Najeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button