Hausa News

Zaɓen gwamna na Kano: APC ta garzaya kotun amma babu Gawuna a shari’ar

Add

Zaɓen gwamna na Kano: APC ta garzaya kotun amma babu Gawuna a shari’ar

Jam’iyyar APC ta shigar da korafi gaban kotun wucin-gadi ta sauraron ƙararrakin zaɓen gwamna na Jihar Kano da ta ayyana zaɓen gwamna, wanda Abba Kabir Yusuf ya lashe, a matsayin wanda ba kammalalle ba, wato inconclusive.

Abba ya lashe zaɓen da ƙuri’u 1,019,602, inda ya doke abokin kararwar sa, Nasiru Yusuf Gawuna da ya samu ƙuri’u 892,705.

A korafin da APC ta shigar a ranar Lahadi da yammaci, ta nuna cewa Abba Yusuf, wanda aka fi sani da Abba Gida-Gida, bai cancanci ma ya shiga zaɓen ba sabo da sunan shi ba ya cikin jerin sunayen mambobin NNPP da aka aike wa INEC.

APC ta kuma ce ita ya kamata a ayayyana ta lashe zaɓen saboda yawancin ƙuri’un da NNPP ta samu ba halastattu ba ne, inda idan aka cire su daga cikin yawan ƙuri’un da aka kada a zaɓen, to tabbas dan takarar ta Hasina ne ke da nasara.

APC ta kuma yi korafin cewa kwamishinan INEC na Kano ya yi kuskure wajen sanar da Abba Gida-Gida a matsayin wanda ya lashe zaɓen duba da cewa tsira ƙuri’un bai haura yawan ƙuri’un da aka kaɗa ba.

Haka kuma APC ɗin ta yi kira ga kotun da ta ayyana Abba Yusuf a matsayin wanda ba dan takara ba sabo da babu sunan shi a rijistar masu zaɓe da aka aike wa INEC a gabanin zaɓen.

Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa ya rawaito cewa jam’iyar ta APC ta cire Gawuna daga ƙarar da ta shigar a gaban kotun.

Sai dai kuma Daily Nigerian Hausa na tunanin cewa mai yuwa hakan ba ya wuce nasaba da taya Abba Yusuf murnar lashe zaɓen da Gawuna din ya yi, inda ya nuna cewa ya yadda da ƙaddara.

Yanzu dai NNPP na da makonni 21 ta amsa ƙorafe-ƙorafe da aka shigar a kan ta daga ranar da aka mika mika mata takardar shigar da ƙarar a kotun.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button