Hausa News

Zaɓɓen gwamnan Kano ya gargadi Ganduje kan amfani da kuɗin gwamnati a zaɓen cike-gurbi

Add

Zaɓɓen gwamnan Kano ya gargadi Ganduje kan amfani da kuɗin gwamnati a zaɓen cike-gurbi

Zababben Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya sake bayar da shawara kan zargin yin amfani da kudaden gwamnati wajen zaben cike-gurbi da za a yi a jihar a gobe Asabar, 15 ga wata.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da babban sakataren yada labarai na zababben gwamnan, Sanusi Dawakin-Tofa ya fitar a yau Juma’a a Kano.

Sanarwar ta ce: “Muna da sahihan bayanai cewa gwamnatin jihar Kano ta bayar da umarnin a saki Naira miliyan 61 ga Doguwa, sama da Naira miliyan 60 ga Nasarawa, sama da Naira miliyan 60 ga kananan hukumomin Wudil domin gudanar da zaben cike-gurbi.

“Yayin da sauran kananan hukumomi kuma aka sanya sunayensu don karbar daruruwan miliyoyin Naira don gudanar da zaben.”

Sanarwar ta ce an fitar da kudin ne kawai domin daukar nauyin ƴan bangar siyasa domin tada zaune tsaye a kan al’umma da mazauna yankin a lokacin da za a sake zaben jihar.

“Muna sake gargadin dukkanin shugabannin kananan hukumomin da ma’aikatan gudanarwar su da su nisanta kansu tare da tabbatar da cewa duk kudaden jama’a da aka saki ba a yi amfani da su ba don haka a tabbata an mayar da su cikin asusun da ya dace,” in ji sanarwar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button