Hausa News

Wasu Daliban Chibok Sun Kubuto Daga Hannun Boko Haram Bayan Kwashe Shekaru Tara A Hannunsu Hausaplay

Add

Bayan kwashe shekaru a hannun Boko Haram, wasu daliban Chibok sun kubuto daga hannun mayakan kungiyar.

Daliban mata su biyu, sun yi nasarar tserewa ne bayan kaimin da sojoji suka kara a baya-bayan nan tare da luguden wuta a kan mayakan na Boko Haram.

A ranar 14 ga watan Afrilun 2014 ne dai aka sace ‘yan matan makarantar Chibok su (276) yayin da allah ya kubutar da wasu daga cikin ‘yan matan daliban dake karatu a makarantar ta Chibok dake maiduguri.

Hakika sace wadannan yan matan daliban da ‘yan bindigar sukayi tamkar hallaka musu rayuwar su, ta duniya da rashin jin dadin rayuwa sukayi sakamakon wata biyan bukata tasu ta karan kansu.

Abin tausayi wasu daga cikin yan matan da yan bindigar suka sace sun aure su badason ransu ba ta hanyar tilasta musu sannan kuma sunci mutuncin wasu daga cikin yan matan a lokacin wasu kuma allah ya basu nasara sun kubuta daga hannun su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button