Hausa News

Sojoji Sun Harbe Barawon Akwatin Zabe A Kebbi

Add

Sai dai wasu mutanen yankin sun yi zargin cewa wakilin jam’iyyar PDP ne.

Sojojin da ke sintirin jiran ko ta kwana sun harbe wani mutum yana kokarin kwace akwatin zabe a hannun jami’an Hukumar Zabe ta Kasa INEC a Jihar Kebbi.

Lamarin na wannan Asabar din da ake karasa Zaben 2023 a wasu sassan jihar ya faru ne a rumfar zabe mai lamba 001 a mazabar Bajida da ke Kudancin Jihar Kebbi.

Bayanai da ke fitowa daga mazauna yankin na cewa marigayin guda ne daga cikin haramtacciyar kungiyar ‘yan sa kai da ke yankin Zuru a jihar.

Wakilinmu ya ruwaito cewa, karar kwana ta cimma mutumin ne wanda ya kutsa cikin rumfar zaben yana mai ikirarin cewa shi jami’in tsaro ne, inda ake zargin har ya yi yunkurin karbar bindigar wani soja a rumfar zaben.

Sai dai wasu mutanen yankin sun yi zargin cewa wakilin jam’iyyar PDP ne.

Wasu kuma dai sun bayyana cewa mutumin tare da wasu masu neman tayar da zaune tsaye sun kutsa rumfar zaben ne suna kokarin kwace akwatunan zabe daga hannun jamian INEC da ke shirin tafiya cibiyar tattara sakamako.

Sai dai kokarin da mutanen wurin suka yi na dakatar da shi ya ci tura, inda ya yi yunkurin karbar bindigar wani soja wanda babu wata-wata wani sojan ya gaggauta diga masa harsashi farat daya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button