Rundunar ƴansanda ta kori jami’an ta da ke tsaron mawaƙi Rarara

Rundunar ƴansanda ta kori jami’an ta da ke tsaron mawaƙi Rarara
Rundunar yansanda ta Ƙasa ta kori wasu jami’ai uku da ke tsaron fitaccen mawakin siyasa na APC ɗin nan, Dauda Kahutu Rarara daga SPU Base 1 Kano, bisa samun su da laifin karya ƙa’idar amfani da makami, rashin da’a, da almubazzarancin harsashi.
A cewar jami’in hulda da jama’a na rundunar, Muyiwa Adejobi, jami’an su uku, Inspr. Dahiru Shuaibu, Sgt. Abdullahi Badamasi, da Sgt. Isah Danladi sun kasance su na aikin tsaron Rarara.
“A yayin da su ke gudanar da aikinsu a ranar Juma’a 7 ga Afrilu, 2023 a kauyen Kahutu da ke Jihar Katsina, jami’an sun yi ta harbin bindiga sama duk da manufofin ‘yan sanda na hana harbe-harbe a iska, sun karya tsarin aiki da kuma yin kunnen uwar Shehu da haɗarin da hakan ka iya haifar wa a cikin taron jama’a a wurin wanda ya hada da kananan yara.
“Halin da su ka aikata ba kawai laifi ba ne da rashin da’a kaɗai, har da ma kuma abin kunya ne ga rundunar da kasa baki daya,” in ji Adejobi a wata sanarwa a ranar Alhamis.
Daily Nigerian Hausa ta tuna cewa a makon da ya gaba ta ne rundunar ta sanar da kama jami’an uku bayan da wani faifan bidiyo ya bayyana, inda ya nuna su suna harba bindiga sama.