Hausa News

Rikicin Sudan: Kamfanin sufurin jiragen sama na Air Peace zai ɗauki nauyin kwaso ƴan Nijeriya kyauta

Add

Rikicin Sudan: Kamfanin sufurin jiragen sama na Air Peace zai ɗauki nauyin kwaso ƴan Nijeriya kyauta

Kamfanin jiragen sama na Air Peace a Najeriya, ya bayyana shirinsa na kwaso ƴan Nijeriya da suka makale a Sudan, Arewa maso Gabashin Afirka kyauta idan har gwamnatin tarayya za ta samar masa da filin sauka da tashin jirgin sama mai aminci da tsaro a kasashen da ke makwabtaka da Sudan.

Shugaban kamfanin, Allen Onyema ne ya bayyana hakan a wata sanarwa a yau Litinin.

A cewarsa, daliban Najeriya da sauran wadanda su ka makale a kasar da ta faɗa yaƙi kwanan nan na bukatar agajin gaggawa.

Onyema ya ce ya zama dole ya taimaka domin kwaso ƴan Nijeriya da su ka makale a kasar da ake gabza yaki, duba da cewa bai kamata Nijeriya ta bari a kashe mata ko mutum daya a Sudan ba.

“Haka kuma, Air Peace a shirye ya ke ya kwashe yan Nijeriya da suka makale a Sudan kyauta idan gwamnati za ta iya kai su filin jirgin sama mai aminci da tsaro a duk kasashen da ke makwabtaka da Sudan. Bai kamata a bar komai a hannun gwamnati kadai ba.

“A shirye muke mu yi cikin gaggawa. Babu bata lokaci. Duk wani aiki da zai inganta martabar kasa, hadin kan kasa, zaman lafiya da hadin kai, to mu ne a ciki

“Har ila yau, ba mu da uzuri na imani da al’ummarmu da kuma son al’ummar kasa duk da wasu kalubalen kasa. Idan aka koma Kenya ko Uganda ko wata ƙasa, za mu shiga don fitar da su. Wasu iyaye sun fara kira gare mu da mu taimaka. A shirye muke mu sake yin haka,” inji shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button