Hausa News
Trending

Nayi Alkawari Taimakon Mutane Dubu Daya Cewar Mawaki Dauda Kahutu Rarara – Hausaplay

hausaplay.com/?p=6137

Add

Shahararren mawaki siyasa a nigeria wanda akafi sani da dauda kahutu rarara ya bayyana cewa yana da wani kuduri da yayi alwashin ganin ya cika a rayuwar shi kafin ya koma ga allah cewar mawaki rarara.

Rarara a cikin jawaban shi ya bayyana cewa zan taimakawa mutane sama da dubu daya ta hanyar Inganta rayuwarsu, kama daga mai bukatar gida, mota, aure, jari Da Sauransu, Inji Mawaki Rarara

Mawakin, wanda ya bayyana hakan a wani bidiyo, ya kuma bukaci jama’a da su taimaka masa da addu’a domin Allah ya ba shi ikon cika wannan burin nasa hakika da za’ana samun mutane irin su rarara da duniya taci gaba cikin kankanin lokaci.

Sannan mawaki ya kara da cewa bada jimawa yakeson ganin ya cimma, wannan burin nasa akan mutanan nigeria marasa karfi dama sauran matasa masu neman ganin an basu tallafin koyon sana’a da sauran su, mawaki rarara yace jama’a suci gaba da taya shi da adu’a don allah.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button