Hausa News
Lauyoyin Mawaƙi Rarara sun bayyana a gaban Kotu

Add
Lauyoyin Mawaƙi Rarara sun bayyana a gaban Kotu
Lauyoyin Mawaƙi Dauda Kahutu Rarara sun bayyana a Kotun Shari’ar Muslunci da ke Rijiyar Zaki a Kano.
Idan zaku iya tunawa wani ɗan kasuwa ne ya yi ƙararar mawaƙin bisa cewa yana binsa bashi kuɗi kimanin Miliyan Goma na wayoyi da yake karɓa yana rabawa mutane.
A zaman Kotun da ya gabata dai Kotun ta bayyana yadda mawaƙin ko lauyoyinsa suka gaza amsa sammacinta.
To amma a Alhamis ɗin nan lauyoyinsa sun bayyana ƙarƙashin Barrister G.A Badawi inda ya nemi a basu damu su yi nazarin tuhume-tuhumen da ake yiwa mawaƙin, domin su yi martani.
Kotun ta sanya ranar Litinin 17 ga watan Afrilun da muke ciki domin ci gaba da wannan shari’ar.