Innalillahi Wa’Inna’ilaihi Raji’un Wasu Yan Bindiga Sunkai Farmaki Jihar Zamfara – Hausaplay

Innalillahi yadsa Al’ummar Yankin Shinkafi Ta Yamma Na Neman Agajin Gaggawa Game Da Matsalar ‘Yan Bindiga dake addabar su, a cikin wasu sassa na jihar zamfara dake nigeria.
Al’ummar yankin na shinkafi sun shaidawa jami’an tsaron yankin cewa ‘yan bindigar da ake zargi da kaiwa al’ummar yankin farmaki dake yankin karamar hukumar shinkafi sun kai farmaki da misalin karfe biyar na ranar juma’ar data gabata a yankin.
Wasu ganau da suka shaidawa manema labarai cewa ‘yan bindigar nada matukar yawan gaske tare da manyan makamai dake hannun su, domin kaiwa jama”ar yankin na shinkafi dake jihar ta zamfara farmaki akan al’ummar yankin jihar.
Tuni dai gwamnatin jihar ta zamfara karkashin jagorancin mai girma gwamna matawalle na jihar ya bayar da umarnin cewa a tsaurara tsattsauran bincike akan lamarin domin ganin an tabbatar da tsaron al’ummar yankin na shinkafi da hare – haren ‘yan bindigar dama jihar ta zamfara baki daya.
Yanzu haka rundunar jami’an tsaron yankin na zamfara sun baza neman ‘yan ta’addan ido rufe domin ganin sun kawo karshen ‘yan ta’addan dake damun al’ummar yankin na jihar ta zamfara dake nigeria, al’ummar yankin na godiya sosai dangane da wannan gudun mawa da gwamnati ta bayar akan su.