Allah Sarki Yadda Wasu Daliban Kasar Nigeria Mazauna Kasar Sudan Suke Tsaka Da Neman Taimakon Gwamnatin Tarayya – Hausaplay

Idan Har Muka Mutu Ba Ku Kawo Mana Dauki Ba Sai Allah Ya Tambaye Ku, Domin Sauran Kasashe Suna Ta Kokarin Ganin Sun Kwashe Mutanensu, Amma Mu Har Yanzu Shiru, Koken Daliban Nijeriya Dake Sudan Zuwa Ga Gwamnatin Nigeria.
Wasu daga cikin daliban nigeria mazauna kasar sudan dake karatu a kasar ta Sudan suna tsaka da neman taimakon gwamnatin kasar mu nigeria yayin da suke cikin wani mawuyacin hali na fama da hare haren da suke fuskanta, a kasar sakamakon fama da rashin zaman lafiya da yake faruwa a kasar.
Yau sama da kimanin kwana hudu (4) kenan kasar ta Sudan ta kasa samun zaman lafiya dalilin rashin fahimtar data faru da ‘yan uwansu dake makwabtaka dasu akan wutar lantarki a kasar ta Sudan wanda dalilin hakan har yanzu an kasa samun ingantaccen zaman lafiya a kasar.
Kasar ta Sudan har kawo yanzu tana fama da rashin zaman lafiya wanda dalilin hakan ya janyo al’ummar kasashe da dama suna ta kaiwa ‘yan kasar su dauki ta hanyar taimakon su, domin ganin sun tseratar da rayuwar su daga wannan mummunan tashin hankalin dake faruwa a kasar ta Sudan.
Yanzu haka daliban kasar nigeria sunfi ko wacce neman ganin an taimaka musu ta hanyar ceton rayuwar su domin ganin an fitar dasu daga kasar da ake neman hallaka su, wata baiwar allah ta bayyana yadda suke tsaka da neman taimakon ganin an fitar dasu a kasar ta Sudan din suna neman adu’a allah ya fitar dasu a wannan hali da suke ciki.