Kannywood
Trending

Adam A Zango Jarumin Kannywood Yayiwa Matar Sa Saki Uku Sakamakon Wasu Dalilai – Hausaplay

hausaplay.com/?p=5803

Add

A karshen ƙarshe, shahararren jarumi kuma mawaƙi a Kannywood, Adam A. Zango, ya saki matar sa, Safiyya Umar Chalawa, watanni biyar bayan ta yi yaji sakamakon rikicin da ya addabi auren nasu.

Da ma ya taɓa sakin ta tun ta na amarya, amma bata kai ga komawa gida ba a lokacin jarumin ya mayar da auren nasu sakamakon kada duniya tasan halin da yake ciki a wannan lokaci.

Wata majiya ta shaida wa wakilin mu cewa da farko Zango ya finjire yace ba zai saki Safiyya ba duk da yake ta sha alwashin ba za ta taɓa komawa gidan sa ba.

Amma sai iyayen ta su ka yanke shawarar kai maganar kotu domin a kashe auren da yaji haka ne ya bata takarda don gudun kar takai su ga anyi fallasa inji majiyar kamar yadda ta rawaito dangane da wannan lamari.

Idan kun tuna, a watan Fabrairu mujallar Fim ta ba ku labarin yadda rikicin da ya turnuƙe tsakanin ma’auratan biyu ya fito fili sakamakon wani bidiyo da Zango ya wallafa a TikTok dangane da yanayin zaman auren sa.

Tuni dai yanzu haka kowa ya kama gaban shi kamar yadda jarumi adam a zango ya bayyana cewa idan har zaman su ya kare shi da safiyya matar shi ta yanzu to maganar gaskiya babu shi babu wani kara aure har abada ko menene ra’ayin ku.

Kuci gaba da kasancewa da shafin mu mai albarka Hausaplay domin samun ingantattun labaran mu kowace rana na gida dana waje kucigaba da kasancewa damu kowani lokaci masoya mungode.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button