Kannywood

Na Dawo Daga Rakiyar Sha’aban, Dukda Ni Na Tsayar Dashi Takara – Rarara

Mawaƙin siyasa a jam’iyyar APC, Dauda Adamu Abdullahi Kahutu Rarara, yace ya dawo daga rakiyar dan takarar gwamnan Kano na jam’iyyar ADP, Sha’aban Ibrahim Sharaɗa, bayan ya gano cewa takarar tasa ta wasa ce ba ta gaske ba.

Rarara ya bayyana haka ne cikin wata tattaunawa da kafar Internet ta DCL Hausa, yana mai cewa shi da kansa ya tsayar ya tsayar da Sha’aban takarar gwamnan Kano, bisa zaton da gaske ake abin, sai daga ya gano cewa Sha’aban ɗin takarar wasa yake.

Hakazalika, Rarara yace sunyi yarjejeniyar za suyi Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a jam’iyyar APC a matakin shugaban ƙasa, amma sai ya fuskanci cewa Sha’aban yana shinshinar jam’iyyar PDP ne, saboda haka ya dawo wajen Dakta Nasiru Yusuf Gawuna na jam’iyyar APC, domin mara masa baya a matsayin dan takarar gwamnan Kano karkashin jam’iyyar APC.

A baya dai, Rarara yace gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya neme shi akan ya goyi bayan Gawuna, amma yace shi Sha’aban zai yi, harma yace a kaf gwamnatin Ganduje, mutum daya ne kawai ya girme shi a bangaren bada gudummawar kafuwar gwamnatin, shi ne Murtala Sule Garo.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button